• Lokacin Da Ya Kamata A Fara Yakin Neman Zaben 2027
    Jan 8 2026

    Send us a text

    A siyasar Najeriya, akwai ka’idoji da dokoki da ke tsara yadda ake gudanar da zaɓe, ciki har da lokacin da doka ta amince a fara yaƙin neman zaɓe. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC, ita ce ke da alhakin bayyana jadawalin zaɓe da kuma ranar da ‘yan takara za su fara neman goyon bayan al’umma a hukumance.


    Sai dai duk da waɗannan tanade-tanade, ana ci gaba da ganin alamu da ayyuka da ke nuna cewa wasu ‘yan takara suna fara yaƙin neman zaɓe tun kafin a buga gangar siyasa.
    Wannan lamari na bayyana ta hanyoyi daban-daban, kama daga yawan tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai, shirya taruka a ɓoye, rabon kayayyaki da kiran jama’a da sunan “taron godiya” ko “ganawar al’umma.


    Shirin Najeriya a yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan lokacin da ya kamata ace an fara gangamin yakin neman zabe.

    Show More Show Less
    10 mins
  • Yaya Matsayar Katsalandar Din Da APC Tace Nyesom Wike Na Yi A Jam’iyyar?
    Jan 7 2026

    Send us a text

    A cikin ‘yan kwanakin nan, siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo, bayan barkewar takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da manyan shugabannin jam’iyyar (APC). Jam’iyyar APC na kallon yadda Wike — wanda ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne amma ke rike da mukami a karkashin gwamnatinta — ke yin katsalandan a harkokin jam’iyyar, musamman a matakin jihohi, a matsayin barazana ga tsarin jam’iyya da ikonta na cikin gida.


    Wannan lamari ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da masu sharhi kan harkokin siyasa.

    Ko wanne matsaya jam’iyyar APC suka dauka kan wannan batu na katsalandan da Nyesom Wike ke yi a jam’iyyarsu?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Show More Show Less
    15 mins
  • Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yanka ‘Yan Kasuwa A Jihar Neja
    Jan 6 2026

    Send us a text

    Harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kasuwar Daji da ke karamar hukumar Borgu a Jihar Neja ya sake jawo hankalin al’umma kan matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a yankunan karkara na Arewa ta Tsakiya. Kasuwar Daji, wadda ke zama cibiyar hada-hadar kasuwanci ga manoma, ‘yan kasuwa da mazauna kauyuka makwabta, ta kasance wuri na zaman lafiya kafin wannan mummunan lamari da ya girgiza mazauna yankin.


    Batutuwa da dama daga kafafen yada labarai da dama sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan batun.

    Ko menene hakikanin abun da ya faru a wannan hari da ‘yan bindiga suka kai a kasuwar Daji?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya a yau na wannan lokaci zai yi duba akai.

    Show More Show Less
    15 mins
  • Sharuddan Da Jam'iyya Za Ta Cika Kafin Kiran Ta Babban Jam'iyyar Adawa
    Jan 2 2026

    Send us a text

    A fagen siyasar Najeriya a halin yanzu, ana ta ce-ce-ku-ce kan wacce ce babbar jam’iyyar adawa da za ta iya tsayawa ƙafada da ƙafada da jam’iyyar APC mai mulki. Wannan takaddama ta fi karkata ne tsakanin jam’iyyar PDP, wacce ta dade tana taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa bayan ficewarta daga mulki a 2015, da kuma jam’iyyar ADC, wacce a ‘yan shekarun nan ta fara samun karɓuwa sakamakon shigar wasu manyan ‘yan siyasa da kuma ƙoƙarin gina sabuwar haɗaka a matsayin madadin tsoffin jam’iyyu.


    Masu goyon bayan PDP na nuna cewa jam’iyyar na da tsari, da tarihi, da kuma gagarumar ƙafar da ta shimfiɗa a kusan dukkan jihohin ƙasar, lamarin da ke ba ta damar kiran kanta babbar jam’iyyar adawa. A ɓangaren guda kuma, magoya bayan ADC na jaddada cewa PDP ta raunana ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida, da yawan sauya sheƙa, da gajiyar da al’umma ke nunawa ga tsoffin jam’iyyun siyasa.
    Kazalika anga yadda manyan jiga-jigan siyasa keta dinkewa wuri daya a jam’iyyar ADC wanda ake ganin ta fara shafe jam’iyyar ta PDP a matsayin babban jam’iyyar adawa a Najeriya.
    Ko me da me ake dubawa don gane babban jam’iyyar adawa a Najeriya?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.

    Show More Show Less
    23 mins
  • Yadda Ya Kamata Ku Gudanar Da Rayuwa A Shekarar 2026
    Jan 1 2026

    Send us a text

    Shekarar 2026 ta zo a wani lokaci da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsin tattalin arziki, da sauye-sauyen siyasa, da kuma ƙalubalen rayuwa da ke bukatar sabon tunani. Wannan ba lokaci ba ne na fatan samun sa’a kawai, lokaci ne na tsara hanya, da ɗaukar matakai, da yin gyara a rayuwar yau da kullum.

    A wannan shiri, za mu duba yadda ya kamata ’yan Najeriya su fara sabuwar shekara ta 2026 ta hanyoyi masu ma’ana—daga kula da yadda zasu sarrafa kuɗi da sana’a, zuwa kiwon lafiya, da siyasa, da uwa uba tsaron rayukan sun.

    shirin Najeriya A Yau ya ji ra’ayoyin masana da kuma shawarwari masu amfani da za su taimaka wa kowa ya fara shekarar da tsari, da hangen nesa, da kuma ƙudurin canji.

    Show More Show Less
    17 mins
  • Siyasa Da Tsare-tsaren Gwamnati Da Suka Dabaibaye 2025
    Dec 30 2025

    Send us a text

    Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, siyasar Najeriya ta kasance cike da sauye-sauye, rikice-rikice, da kuma manyan al’amura da suka shafi iko, jam’iyyu da shugabanci. Shekarar ta shaida sauyin sheƙa na ‘yan siyasa, rikicin cikin gida a wasu jam’iyyu, da kuma fafutukar karɓar ragamar mulki a jihohi da matakin tarayya, lamarin da ya ƙara zafafa siyasar ƙasa.

    A bangaren tsare-tsaren gwamnati kuwa, 2025 ta kasance shekara mai ɗauke da tsauraran manufofi da suka shafi tattalin arziki, tsaro da walwalar al’umma. Gwamnati ta ɗauki matakai masu nauyi domin tinkarar matsalolin tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauye-sauyen tattalin arziki, inda wasu tsare-tsaren suka samu karɓuwa, wasu kuma suka jawo muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan kasa.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi waiwaye ne kan siyasa da tsare-tsaren gwamnati da suka dabaibaye shekarar 2025 da muke bankawana da ita.

    Show More Show Less
    22 mins
  • Waiwaye Kan Manyan Kalubalen Tsaro Da Suka Faru A 2025
    Dec 29 2025

    Send us a text

    A shekarar 2025, Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro da suka fi daukar hankali, musamman hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ta’addanci a jihohin Arewa kamar Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Borno. Hare-haren sun yi sanadin rasa rayuka, da rufe makarantu, da kaura daga gidaje, da kuma durkushewar harkokin tattalin arziki a wasu yankuna.


    Wadannan matsaloli suka sa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro, domin daukar matakan gaggawa na kare rayuka da dawo da doka da oda wanda hakan yasa shugaban kasa dawo da tsohon babban hafsan rundunar sojin Najeriya a matsayin ministan tsaro.


    Shirin Najeriya a yau na wannan lokaci zai yi waiwaye ne kan manyan kalubalen tsaro da suka faru a 2025.

    Show More Show Less
    19 mins
  • Yadda Kiristoci Ke Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Cikin Musulmi
    Dec 26 2025

    Send us a text

    A duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa.

    A wurare da dama kamar Kaduna, Jos, Zaria, Minna da wasu sassan jihar Kano, ana ganin Kiristoci suna zuwa coci ba tare da tsangwama ba, yara suna yin nishadi tare, makwabta suna raba abinci da gaisuwar biki. Wannan yanayi na nuna cewa zaman lafiya, girmamawa da zumunci sun fi bambancin addini ƙarfi a rayuwar yau da kullum ta Arewacin Najeriya.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda kiristoci ke gudanar da bikin kirsimeti a tsakiyar musulmai.

    Show More Show Less
    17 mins